Shugabannin Iran na kokarin gabatar da sabuwar yarjejeniyar fahimtar juna da Amurka
Shugabannin Iran na kokarin gabatar da sabuwar yarjejeniyar fahimtar juna da Amurka a matsayin nasarar da suka samu bayan tsayin daka da gwagwarmaya, duk da cewa kasar ta fuskanci kalubale masu yawa sakamakon yaki, takunkuman tattalin arziki da matsin lamba daga cikin gida.
Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Bagher Qalibaf, ya bayyana cewa yarjejeniyar ta kasance babban mataki zuwa ga nasara, yayin da Shugaba Masoud Pezeshkian ya ce idan aka aiwatar da ita gaba daya, za ta iya magance matsaloli da dama tare da kawo sauyi mai kyau ga Iran da Gabas ta Tsakiya.
Mahukuntan Iran na ganin yarjejeniyar a matsayin nasara saboda, a cewarsu, Amurka da Isra’ila sun kasa cimma manyan manufofinsu na tilasta wa Iran mika wuya, rushe gwamnatin kasar ko kawo karshen shirinta na nukiliya ta hanyar karfin soja.
Sai dai wasu masu ra’ayin rikau a cikin gwamnatin Iran sun nuna adawa da yarjejeniyar, suna masu cewa za ta iya bai wa Amurka tasiri mai yawa kan harkokin kasar.
Har yanzu dai muhimman batutuwa kamar shirye-shiryen nukiliyar Iran, sassauta takunkumai da batun mashigir Hormuz na jiran tattaunawa a wani taro da ake sa ran gudanarwa a kasar Switzerland.
