Kotun Daukaka Kara ta Dakatar da hukuncin Babban Kotu na soke Rajistar Jam'iyyar ADC

Kotun ɗaukaka ka ƙara a Najeriya ta bada umarni gaggauta dakatar da aiwatar da hukuncin wata babbar kotun Abuja na soke wasu jam’iyyun adawar ƙasar guda biyar, cikin su harda ADC saboda zargin saɓa ƙa’idar dokokin zaɓe.

Alkalan kotun guda uku sun bai wa hukumar zaɓe ta INEC umarnin dakatar da shirin soke jam’iyyun tare da zargin alkalin babbar kotun Peter Lifu da ƙin mutunta umarnin kotun ɗaukaka ƙara da kuma yin gaban kan sa dangane da hukuncin.

Alkalan sun ce sun bada wannan umarni ne har zuwa lokacin da za su saurari ƙarar dake gaban su dangane da ita shari’ar da aka yi a gaban alkali Lifu domin yanke hukunci.

Tuni hukuncin Lifun ya haifar da fargaba da kuma cece kuce dangane da makomar jam’iyyun adawan guda biyar da suka haɗa da ADC da Accord da AA da ZLP da kuma APP, waɗanda ke shirin zaɓen shekarar mai zuwa.

A martanin sa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, kuma ɗan takaran shugaban ƙasa a Jam’iyyar ADC, ya bayyana farin cikin sa dangane da umarnin kotun ɗaukaka ƙarar.

Atiku ya kuma yabawa hukumar zabe ta INEC wadda ita ma ta buƙaci dakatar da aiwatar da hukuncin babbar kotun na neman soke jam’iyyun guda biyar.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url