Dole Ne Afirka Ta Jagoranci Magance Barazanar Tsaro da Ke Ƙaruwa – Buratai
Tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya), ya yi kira ga ƙasashen Afirka da su jagoranci samar da mafita ga matsalolin tsaro da ke ƙara ta'azzara a nahiyar, yana mai gargadin cewa Afirka na fuskantar taruwar barazana iri-iri da ba a taɓa ganin irinta ba, wanda ke buƙatar haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen nahiyar.
Buratai ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a yayin da yake gabatar da muhimmin jawabi mai taken "Muhimman Barazanar Tsaro da Afirka Ke Fuskanta" a taron Parliamentary Intelligence-Security Forum karo na 32 da aka gudanar a Addis Ababa, babban birnin Habasha.
Ya bayyana manyan matsalolin tsaro guda biyar da ke addabar nahiyar, waɗanda suka haɗa da:
- Ta'addanci da tsattsauran ra'ayi,
- Manyan laifuffukan da ke ƙetare iyakokin ƙasashe,
- Barazanar hare-haren intanet (cybersecurity),
- Rashin kwanciyar hankali sakamakon matsalolin shugabanci,
- Da kuma raunana ikon cin gashin kai sakamakon dogaro da ƙasashen waje.
A cewarsa, lokaci ya yi da Afirka za ta daina dogaro da tsoma bakin ƙasashen waje kaɗai, ta kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe, musayar bayanan sirri da kuma bunƙasa ƙarfin hukumomin tsaron cikin gida.
Buratai ya bayyana yankin Sahel a matsayin cibiyar ta'addanci mafi muni a duniya, yana mai cewa yankin na ɗaukar kusan rabin adadin mutanen da ake kashewa sakamakon hare-haren ta'addanci a faɗin duniya.
Ya ce tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamban shekarar 2025, yankin Yammacin Afirka ya fuskanci kimanin hare-haren ta'addanci 450, waɗanda suka yi sanadin mutuwar sama da mutane 1,900.
Tsohon hafsan sojin ya kuma ce duk da nasarorin da gwamnatin Burkina Faso ƙarƙashin Shugaba Ibrahim Traoré ta samu wajen ƙwato kusan kashi 72.7 cikin 100 na yankunan da 'yan ta'adda suka mamaye zuwa watan Yunin 2025 ta hanyar Operation Lalmassga, ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi na ci gaba da kai munanan hare-hare.
Ya ƙara da cewa hare-haren soji da aka ƙara kaimi a farkon shekarar 2026 sun yi sanadin kashe aƙalla mayaƙa 400, amma sabbin hare-haren da ƙungiyoyin masu alaƙa da Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) suka kai sun nuna cewa barazanar ta'addanci har yanzu tana nan daram.
Buratai ya kuma nuna damuwa kan ficewar Burkina Faso, Mali da Nijar daga ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), yana mai cewa hakan ya raunana musayar bayanan sirri da ƙoƙarin haɗin gwiwa wajen tabbatar da tsaro a yankin.
Ya yi gargadin cewa matsalar tsattsauran ra'ayi da ta'addanci na ci gaba da bazuwa daga yankin Sahel zuwa ƙasashen gabar tekun Yammacin Afirka, yana misalta ƙaruwar hare-hare da aka samu a arewacin ƙasar Benin cikin shekaru uku da suka gabata.
Game da manyan laifuffukan da ke ƙetare iyakokin ƙasashe, Buratai ya ce Yammacin Afirka na fuskantar haɗaɗɗun barazana da suka haɗa da ɗaukar nauyin ta'addanci, fashin teku, safarar makamai, safarar miyagun ƙwayoyi da kuma laifuffukan intanet.
Ya bayyana cewa ƙungiyoyin masu aikata irin waɗannan laifuffuka na ƙara amfani da fasahohin zamani, raunin kula da iyakoki da kuma gazawar tsarin mulki wajen faɗaɗa ayyukansu a yankin.
Har ila yau, Buratai ya bayyana tsaron intanet a matsayin wata sabuwar babbar barazana ga tsaron ƙasa, yana mai kira ga ƙasashen Afirka da su saka hannun jari wajen ƙarfafa kariyar intanet, kare cibiyoyin fasahar sadarwa da kuma ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen nahiyar.
A ƙarshe, ya buƙaci gwamnatocin Afirka, masu tsara manufofi da hukumomin tsaro da su rungumi dabarun da nahiyar ta samar da kanta domin fuskantar sauye-sauyen barazanar tsaro, tare da kare ikon cin gashin kai da kuma samar da zaman lafiya mai ɗorewa da ci gaba.
Ya jaddada cewa samun cikakken tsaro a Afirka ba zai yiwu ba sai an ƙarfafa hukumomi, an bunƙasa haɗin gwiwar musayar bayanan sirri, an inganta ƙarfin tattalin arziki, tare da ƙara jajircewar shugabannin ƙasashen nahiyar wajen aiki tare.
