Jami'an Tsaro Sun Hallaka Sama da 'Yan Bindiga 40, Sun Daƙile Babban Hari a Katsina

 


Jami'an tsaro sun samu gagarumar nasara bayan sun daƙile wani babban hari da ɗaruruwan 'yan bindiga suka kai garin Guga da ke Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, inda aka kashe sama da 'yan bindiga 40 tare da wasu daga cikin manyan kwamandojinsu.

Kwamishinan Tsaron Jihar Katsina, Dr. Nasir Mu'azu, ya bayyana cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:40 na yammacin ranar Lahadi, 26 ga Yulin 2026, lokacin da sama da 'yan bindiga 200 ƙarƙashin jagorancin fitaccen shugaban 'yan bindiga, Idi Abasu Aiki, tare da wasu mayaƙan ƙungiyar Ado Aleru daga Jihar Zamfara suka kai farmaki domin ramuwar gayya.

Ya ce jami'an tsaro sun samu sahihan bayanan sirri tun kafin harin, lamarin da ya ba su damar shirya kariya tare da mayar da martani cikin gaggawa.

A cewarsa, arangamar ta tilasta wa maharan ja da baya bayan sun yi asarar sama da mutum 40, yayin da bayanan sirri suka tabbatar da cewa kusan manyan kwamandojin 'yan bindiga takwas sun mutu a farmakin.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa shugaban harin, Idi Abasu Aiki, ya samu munanan raunukan harbin bindiga, lamarin da ake ganin zai ƙara raunana ƙungiyarsa.

Bayan daƙile harin, jami'an tsaro sun fara aikin share yankin domin kwato makamai da sauran kayan aikin da 'yan bindigar suka bari a filin daga, tare da ƙara tsaurara sintiri da sa ido domin hana sake kai irin wannan hari.

Sai dai gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa mambobin ƙungiyar mafarauta huɗu sun rasa rayukansu yayin arangamar. Rahotanni sun nuna cewa mafarautan na daga cikin waɗanda suka taimaka wajen kare al'umma a lokacin da aka kai harin.

Gwamnatin Katsina ta yaba da ƙoƙarin jami'an tsaro da sauran masu ba da gudummawar tsaro, tana mai tabbatar da cewa za ta ci gaba da haɗa kai da hukumomin tsaro domin murƙushe 'yan bindiga da dawo da zaman lafiya a faɗin jihar.

Ta kuma yi kira ga al'umma su ci gaba da bai wa jami'an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen yaƙi da matsalar tsaro da ke addabar wasu yankunan jihar.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url