GWamnatin Tarayya Ta Ware Kusan N962.8bn Don Motocin SUV da Shirye-shiryen Tallafa wa Jama'a a Kasafin Kuɗin 2026

 


Bincike kan kasafin kuɗin Tarayyar Najeriya na shekarar 2026 ya nuna cewa an ware jimillar N962.83 biliyan domin sayen motocin Sport Utility Vehicles (SUVs) da kuma aiwatar da shirye-shiryen tallafa wa jama'a.

Rahoton da ƙungiyar sa ido kan kasafin kuɗi ta Tracka ta fitar ya nuna cewa N15.13 biliyan daga cikin kuɗin an ware shi ne domin sayen motocin SUV guda 39, yayin da N947.70 biliyan aka tanada domin aiwatar da ayyukan tallafa wa jama'a guda 2,579.

Tracka ta bayyana cewa adadin kuɗin da aka ware ya zarce jimillar kasafin wasu manyan ma'aikatun gwamnatin tarayya guda bakwai. Sai dai ƙungiyar ta nuna damuwa cewa ayyukan tallafa wa jama'a da dama ba su da takamaiman wuraren aiwatarwa, wanda zai iya sa ya yi wuya ga jama'a da hukumomin sa ido su tantance yadda ake aiwatar da su.

Rahoton ya kuma nuna cewa ayyukan sun bazu a hukumomi 184, ciki har da wasu cibiyoyi da ba su da alhakin gudanar da irin waɗannan shirye-shirye. Tracka ta ce irin wannan tsarin na iya rage gaskiya da riƙon amana wajen kashe kuɗaɗen gwamnati.

Ƙungiyar ta kuma yi nuni da cewa wannan ware kuɗi na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke shirin dogaro da bashin kuɗi wajen cike gibin kasafin kuɗin shekarar 2026. A cewarta, ya kamata a fifita ayyukan da ke da tasiri kai tsaye ga ci gaban tattalin arziki da jin daɗin al'umma, tare da tabbatar da cikakkiyar gaskiya da sauƙaƙa wa jama'a damar bibiyar yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url