Alhaji (Dr.) Salihu Abdullahi Muhammad Ya Zama Sakataren Ƙasa na Ƙasa na Haɗa Ilimin Tsangaya da Tsarin Ilimi na Zamani



An naɗa Alhaji (Dr.) Salihu Abdullahi Muhammad (Jarman Kumo) a matsayin Sakataren Ƙasa na na Haɗa Ilimin Tsangaya da Tsarin Ilimi na Zamani

Naɗin na daga cikin matakan ƙarfafa shugabancin shirin da ke da burin inganta tsarin ilimin Tsangaya ta hanyar haɗa shi da ilimin zamani da kuma bunƙasa damar ilimi ga ɗalibai a faɗin ƙasar.

Ana sa ran sabon Sakataren Ƙasar zai yi aiki tare da sauran shugabannin shirin wajen tsara manufofi da aiwatar da shirye-shiryen da za su inganta ilimin Tsangaya, ƙarfafa malamai da ɗalibai, tare da tallafa wa ci gaban ilimi a Najeriya.

Masu ruwa da tsaki a fannin ilimi sun bayyana fatan cewa ƙwarewa da gogewar Alhaji (Dr.) Salihu Abdullahi Muhammad za su taimaka wajen cimma manufofin shirin da ƙara bunƙasa tsarin ilimin Tsangaya a ƙasa baki ɗaya.

Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url