Zaɓen 2027: Ƴan Takarar APC a Gombe Sun Karɓi Fom ɗin INEC
Dukkanin ‘Yan takarar na Jam’iyyar APC sun karbi takarnun izinin neman tsayawa Takara na Hukumar zabe mai cin gashin Kan ta wato INEC abunda ke tabbatar da cewa su ne jam’iyyar ta amince su ma mata Takara a Zabukan shekara ta 2027 a jihar Gombe
Tun daga dan takararta na gwamna zuwa na Majalisar Dokokin
Ƙasa da na jiha ne suka karɓi fom ɗin takara na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta
Ƙasa, INEC, a matsayin waɗanda aka tabbatar a hukumance a matsayin masu tutar
jam’iyyar.
An gudanar da bikin miƙa fom ɗin ne a Fadar Gwamnatin Jihar
Gombe, inda Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranci bayar da fom ɗin ga ‘yan
takarar, yana mai bayyana matakin a matsayin kammala tsarin fidda ‘yan takara
na cikin gida da kuma fara matakan doka na miƙa sunayensu ga INEC.
Daga cikin waɗanda suka karɓi fom ɗin akwai ɗan takarar
gwamnan APC, Dakta Jamilu Isiyaku Gwamna, wanda ya fito a matsayin wanda ya
lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.
Haka kuma an miƙa fom ɗin ga ‘yan takarar Sanata da suka haɗa
da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya mai neman wakiltar yankin Gombe ta Arewa, DCP
Ahmed Mohammed Deba mai ritaya na Gombe ta Tsakiya da kuma Honarabul Jerry
Joseph Damara na Gombe ta Kudu.
Har ila yau, ‘yan takarar kujerun Majalisar Wakilai guda
shida na jam’iyyar su ma sun karɓi fom ɗin nasu.
Da yake jawabi yayin taron, Gwamna Inuwa Yahaya ya taya ‘yan
takarar murna bisa samun amincewar shugabanci da mambobin jam’iyyar, yana mai
kira gare su da su ɗauki nasarar tasu a matsayin ƙarin nauyi na yi wa al’umma
hidima.
Ya bayyana cewa karɓar fom ɗin INEC na nuna wani muhimmin
mataki a tsarin zaɓe, inda ake sa ran ‘yan takarar za su cika duk wasu takardu
da ake buƙata bisa dokar zaɓe da ƙa’idojin INEC.
Gwamnan ya kuma buƙaci ‘yan takarar su ci gaba da haɗin kai
da jajircewa yayin da jam’iyyar ke shirin shiga sabon mataki na shirye-shiryen
zaɓe.
Ya nuna kwarin gwiwa cewa ɗan takarar gwamna Dakta Jamilu
Gwamna da sauran ‘yan takarar Majalisar Dokokin Ƙasa suna da ƙwarewa da gogewar
da za su iya wakiltar muradun al’ummar jihar da ƙasa baki ɗaya.
Matakin miƙa fom ɗin dai ya nuna kammala dukkan matakan
cikin gida da suka shafi fitowar ‘yan takarar APC a jihar Gombe gabanin zaɓen
shekarar 2027.



