Manyan Kwamandojin ISWAP Sun Miƙa Wuya Yayin da Sojoji Ke Ƙara Matsin Lamba
Rundunar sojin Najeriya ta sake bayyana samun wata gagarumar nasara a yaƙin da take yi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas bayan da wasu manyan jagororin ƙungiyar ISWAP suka miƙa wuya ga dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation HADIN KAI. Haka kuma mayaka 76 tare da wasu daga cikin iyalansu sun ajiye makamansu a cikin makon da ya gabata.
Rahotanni sun nuna cewa wannan ci gaba ya biyo bayan ci gaba da kai hare-hare masu ƙarfi da jami’an tsaro ke yi kan maboyar ‘yan ta’adda tare da amfani da sahihan bayanan sirri domin kai farmaki a wuraren da ake zargin ‘yan ta’addan ke ɓuya.
Mukaddashin jami’in yaɗa bayanai na rundunar haɗin gwiwa ta Operation HADIN KAI, Kyaftin Mohammed Goni, ya bayyana cewa ci gaba da gudanar da hare-hare da amfani da bayanan sirri masu inganci na ci gaba da haifar da sakamako mai kyau a yaƙin da ake yi da Boko Haram da ISWAP.
Ya ce jami’an tsaro sun samu nasarar tarwatsa sansanonin ‘yan ta’adda tare da rage musu damar motsi da hanyoyin samun kayan aiki, lamarin da ya janyo raguwar ƙarfin mayakan da kuma raunin jagorancinsu.
Sai dai jami’an tsaron ba su bayyana sunayen manyan kwamandojin da suka miƙa wuya ba ko kuma inda suka fito saboda dalilan tsaro. Haka kuma sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike da tattara bayanai a kansu bisa ƙa’idojin aiki da aka tanada.
Masana harkokin tsaro na ganin cewa miƙa wuya da manyan jagororin ƙungiyoyin ta’addanci ke yi na nuna tasirin dabarun da jami’an tsaro ke amfani da su. Sai dai sun ce akwai buƙatar ci gaba da matsin lamba da kuma haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da al’umma domin tabbatar da dorewar nasarorin da ake samu.
Wasu masu sharhi kuma sun ce duk da irin waɗannan nasarori, ya zama wajibi a tabbatar da bin hanyoyin tantance waɗanda suka miƙa wuya tare da shirye-shiryen gyaran hali da sake dawo da su cikin al’umma yadda ya kamata.
Rundunar Operation HADIN KAI ta jaddada cewa za ta ci gaba da matsin lamba kan sauran ‘yan ta’addan har sai an kawo ƙarshen ayyukansu tare da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin Arewa maso Gabas.

