Dickson da Kwankwaso Sun Gana Yayin da Rikicin Siyasar NDC Ke Ƙara Ɗaukar Hankali

 An fara nuna sabuwar damuwa kan yanayin siyasa da tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya bayan da jam’iyyar Nigeria Democratic Congress, NDC, ta zargi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, da hana ta damar shiga tsarin miƙa sunayen ‘yan takara gabanin babban zaɓen shekarar 2027.




Jam’iyyar ta ce rashin samun lambar shiga tsarin na’urar sadarwa ta hukumar zaɓen ya hana ta cike bayanai da kuma miƙa sunayen ‘yan takararta cikin lokacin da aka tanada.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da takun-saka tsakanin jam’iyyar da hukumar zaɓe, bayan wata kotun tarayya da ke Lokoja ta soke wani hukunci na baya da ya umarci INEC ta yi wa jam’iyyar rajista.

A hukuncin da Mai Shari’a Isah Dashen ya yanke, kotun ta bayyana cewa hukuncin da aka yanke a baya bai bi ƙa’ida ba, saboda ba a saurari dukkan bangarorin da lamarin ya shafa ba kafin yanke hukunci.

Rahotanni sun nuna cewa matakin ya biyo bayan ƙarar da jam’iyyar Peace Movement Party, PMP, ta shigar, inda ta yi zargin cewa tana da ruwa da tsaki a lamarin amma ba a shigar da ita cikin shari’ar ba.

A wani sabon ci gaba kuma, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya gana da jagoran jam’iyyar Seriake Dickson a Abuja.

Ko da yake ba a bayyana cikakken abin da suka tattauna ba, masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin ganawar na zuwa ne a lokacin da jam’iyyar ke fuskantar ƙalubalen shari’a da kuma batutuwan da suka shafi shirye-shiryen zaɓe.

Sai dai wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin jama’a da masu fafutukar dimokuraɗiyya sun yi kira ga hukumomi da su tabbatar da adalci da bai wa dukkan jam’iyyun siyasa damar shiga harkokin siyasa ba tare da nuna son kai ba.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, INEC ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye dangane da zargin da NDC ta yi ba.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url