Dakarun Operation FANSAN YAMMA Sun Ceto Mutane 48 Bayan Dakile Harin 'Yan Bindiga a Zamfara
Dakarun Rundunar Hadin Gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA sun dakile wani hari da 'yan bindiga suka kai ƙauyen Magami da ke Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara, inda suka samu nasarar ceto mutane 48 da aka yi garkuwa da su.
A cewar rundunar, maharan sun kutsa cikin ƙauyen ne da babura masu yawa domin sace mazauna yankin. Bayan samun rahoton gaggawa, dakarun soji sun isa wurin tare da fafatawa da maharan, lamarin da ya tilasta musu tserewa tare da barin mutanen da suka sace.
Rundunar ta bayyana cewa an mika mutanen da aka ceto ga hukumomin da suka dace domin kula da lafiyarsu da kuma haɗa su da iyalansu.
Masu ruwa da tsaki na ci gaba da yabawa dakarun tsaro kan wannan nasara, yayin da ake kira ga ci gaba da ƙarfafa ayyukan leƙen asiri da haɗin kan al'umma domin magance matsalar 'yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma.
