Gwamnatin Bauchi Ta Musanta Jita-jitar Kayyade Sadakin Naira 1,500 Ga Matan da Aka Saki

 


Gwamnatin Jihar Bauchi ta musanta wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta wanda ke ikirarin cewa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya amince da kayyade sadakin matan da aka saki a kan Naira 1,500.

Kwamishinan Harkokin Addini da Wayar da Kai na jihar, Injiniya Muhammad Binni Abdulkadir, ya bayyana cewa wannan ikirari ƙarya ne, marar tushe kuma an ƙirƙire shi ne domin yaudarar jama'a. Ya jaddada cewa gwamnatin Bauchi ba ta taɓa fitar da wata doka ko tsari da ya shafi kayyade sadakin mata ba.

Gwamnatin ta bukaci al'umma su yi watsi da wannan jita-jita, tare da tabbatar da sahihancin duk wani bayani kafin yaɗa shi a kafafen sada zumunta.

Ta kuma yi gargadin cewa yaɗa labaran ƙarya na iya haifar da ruɗani, tada hankalin jama'a da kuma kawo cikas ga zaman lafiya da haɗin kan al'umma.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url