Mai Mala Buni, ya na shan Caccaka bayan ya yi alkawarin bayar da Naira miliyan 300 domin tallafa wa aikin jami’ar JIBWIS

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya fuskanci suka kan alkawarin bayar da Naira miliyan 300 daga aljihunsa domin tallafa wa jami’ar da ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ke shirin ginawa.

Ce-ce-ku-cen ya biyo bayan halartar gwamnan wani taron karawa juna sani na JIBWIS a Jos, Jihar Plateau, ranar Lahadi. A wajen taron ne Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa, Kabiru Masari, ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 300 daga aljihunsa, tare da yin wani alkawarin Naira miliyan 300 a madadin Gwamna Buni.

Lamarin ya haifar da martani a kafafen sada zumunta, inda wasu mazauna Yobe da masu fafutuka suka fara tambayar dacewar gwamnan ɗaukar nauyin irin wannan adadi ga wata cibiyar addini, musamman a lokacin da ake fuskantar ƙalubale a fannonin ilimi, lafiya da sauran muhimman sassa na jihar.

Sai dai Gwamnatin Jihar Yobe ta fayyace cewa alkawarin gudummawar na Buni ne da kansa, ba a madadin Gwamnatin Jihar Yobe ba.

A cikin wata sanarwa, Darakta-Janar na Yaɗa Labarai da Harkokin Watsa Labarai na Gwamnan, Mamman Mohammed, ya ce Buni ya halarci taron tare da gwamnonin Kano, Sokoto da Jigawa, wato Abba Kabir Yusuf, Ahmed Aliyu da Umar Namadi, da kuma Kabiru Masari da sauran manyan baƙi.

A cewarsa, tawagar ta fara kai wa Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, ziyarar ban-girma kafin daga bisani ta wuce wajen taron.

Mohammed ya ce an gayyaci manyan mutanen ne domin su gabatar da saƙonnin fatan alheri a taron, inda Buni ya yi nasa jawabin kafin Kabiru Masari.

Ya ce a lokacin da Masari ke kammala jawabinsa, ya sanar da cewa an gaya masa cewa JIBWIS na gina jami’a, sannan ya yi alkawarin bayar da Naira miliyan 300 da kansa, tare da wani Naira miliyan 300 a madadin Buni.

“Domin kauce wa ruɗani da kuma fayyace lamarin, gudummawar da Hon. Masari ya yi a madadin kansa da kuma Gwamna Buni gudummawa ce ta kashin kai, ba a madadin Gwamnatin Jihar Yobe ba,” in ji Mohammed.

Ya ƙara da cewa Masari ba shi da ikon yin wani alkawari ko ɗaukar wata shawara a madadin Gwamnatin Jihar Yobe.

Ya ce saboda haka, ba gaskiya ba ne, kuma yaudara ce ko karkatar da gaskiya, a ce ko a ba da ra’ayin cewa alkawarin da Masari ya yi a madadin kansa da Buni na nufin za a biya kuɗin ne daga albarkatun Gwamnatin Jihar Yobe.

Sukan da aka yi

Kafin wannan bayani daga gwamnati, wasu mazauna jihar da masu fafutuka sun soki gudummawar, suna tambayar ko ba za a iya amfani da irin wannan kuɗi wajen magance wasu matsalolin jihar ba.

Wani ɗan jam’iyyar PDP a Yobe, Umar Yobe, ya soki gudummawar, yana zargin cewa ana amfani da kuɗin gwamnati wajen aikin.

Ya ce:

“An bayar da Naira miliyan 300 cikin sakaci ga aikin Sheikh Jingir daga baitul malin gwamnati ba tare da amincewar kowa ba. Ba zai iya bayar da ko kaso kaɗan na wannan adadin ba idan ba ya kan madafun iko. Haka wasu ke amfani da iko ta hanyar da ba ta dace ba.”

Wani mai fafutuka, KY Tebo, ya kuma nuna damuwa kan matsalolin kiwon lafiya, musamman cututtukan da suka shafi ƙoda, waɗanda ya ce suna addabar mazauna ƙananan hukumomin Bade da Jakusko.

Ya ce:

“Cutar ƙoda na kashe mazauna Bade da Jakusko, yayin da gwamnan ya kasa gina cibiyar wankin ƙoda.”

Tebo ya ce batun ba wai adawa da addini ko jami’ar da ake shirin ginawa ba ne, sai dai batun fifikon abubuwan da gwamnati ya kamata ta mayar da hankali a kai.

Wani mai fafutuka, Adamu Bello Jana, ya ce fannin ilimi ma na buƙatar ƙarin kulawa, musamman wajen gyaran makarantun da suka lalace da kuma rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar.

Ya ce:

“Fannin ilimi na daga cikin mafi munin fannoni a jihar, kuma wannan shi ne abin da ya kamata gwamnati ta ba muhimmiyar kulawa.”

Ya ƙara da cewa akwai makarantu da dama da ke cikin mummunan yanayi kuma suke buƙatar gyara cikin gaggawa.

“Muna da yara da yawa da ba sa zuwa makaranta a Yobe, amma maimakon mu ga zuba jari mai ƙarfi a ilimi, muna ci gaba da ganin makarantu da suka lalace,” in ji shi.


Bayan bayanin da gwamnatin jihar ta yi, batun ya koma daga tambayar ko an yi amfani da kuɗin Gwamnatin Yobe wajen yin alkawarin, zuwa tambayar ko ya dace gwamna ya bayar da irin wannan babban tallafi daga aljihunsa, a matsayinsa na ɗan ƙasa, a lokacin da ake fuskantar ƙalubale a harkokin ilimi da lafiya a jihar.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url