RUWASSA Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Cibiyoyin Lafiya Uku A Gombe
Hukumar Samar da Ruwa da Tsaftar Muhalli a Ƙauyuka ta Jihar Gombe, RUWASSA, ta raba magunguna da kayan aikin lafiya kyauta ga cibiyoyin kula da lafiya guda uku da ke ƙananan hukumomin Akko, Balanga da Dukku, domin inganta ayyukan kiwon lafiya a matakin al’umma.
Cibiyoyin da suka amfana da tallafin su ne cibiyar lafiya ta Garko da ke Akko, Bangu da ke Balanga, da kuma Gombe Abba da ke ƙaramar hukumar Dukku.
Babban Manajan hukumar, Injiniya Muhammad Gibriumu Ahmad, ya samu wakilcin Jami’in Gudanarwa na hukumar, Adamu Buji, wanda ya jagoranci rabon kayayyakin.
A ƙaramar hukumar Balanga, shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Salisu Ibrahim, ya tabbatar da cewa za a sanya ido kan rabawa da amfani da magungunan, ta hannun mai kula da cibiyoyin lafiya na ƙaramar hukumar, Mista Danjuma K. Mauni.
Haka kuma, shugaban gundumar Bangu, Alhaji Danjuma Sulaiman, wanda Malam Aliyu Gwadabe ya wakilta, ya yi alƙawarin tabbatar da amfani da magungunan yadda ya kamata, musamman wajen taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi.
Hukumar RUWASSA ta bayyana aniyarta ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen da za su inganta lafiyar al’umma da kyautata rayuwar mazauna jihar.
