Rundunar 'Yan Sanda sun tabbatar da Mayakan ISWAP Sun Kai Hari Makaranta a Borno, Sun Yi Garkuwa da Ɗalibai Masu Rubuta Jarabawar NECO



An sake samun tashin hankali a jihar Borno bayan wasu da ake zargin mayakan ƙungiyar ISWAP ne sun kai hari wata makarantar sakandaren gwamnati da ke garin Lassa a ƙaramar hukumar Askira-Uba, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da dama tare da kashe wani malami.

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta tabbatar da faruwar lamarin, inda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Nahum Kenneth Daso, ya bayyana cewa maharan sun kutsa cikin garin ne a kan babura a ranar kasuwa, lamarin da ya ba su damar shiga yankin ba tare da an yi zargin wani abu ba.

A cewarsa, bayan shiga garin, maharan sun nufi makarantar Government Day Secondary School da ke Lassa, inda suka buɗe wuta domin tayar da hankalin mutane kafin su shiga azuzuwan makarantar.

Ya ce maharan sun kashe wani malami tare da tafiya da ɗaliban da suke cikin azuzuwansu a lokacin harin.

Sai dai jami’in ya ƙara da cewa dakarun tsaro sun yi artabu da maharan, abin da ya taimaka wajen rage girman barnar da ka iya faruwa.

Majiyoyin yankin sun ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe tara na safe, a daidai lokacin da wasu ɗaliban aji na ƙarshe ke rubuta jarabawar kammala sakandare ta NECO.

Rahotanni sun nuna cewa bayan buɗe wuta a makarantar, maharan sun shiga wuraren rubuta jarabawa tare da tafiya da wasu ɗalibai da malamai zuwa wani wuri da ba a san inda yake ba.

A halin yanzu jami’an tsaro na ci gaba da sintiri da kuma bincike a dazukan da ke kewaye da yankin domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su da kuma cafke waɗanda suka kai harin.

Lamarin na zuwa ne kwanaki 47 bayan wasu ɗalibai 42 daga makarantar Mussa Primary da Junior Secondary School a wannan ƙaramar hukuma ta Askira-Uba suka faɗa hannun masu garkuwa da mutane.

Iyalan waɗancan ɗaliban sun bayyana damuwarsu, suna cewa har yanzu ba su samu wani saƙo daga masu garkuwa da mutanen ba, abin da ke ƙara jefa su cikin fargaba kan halin da ‘ya’yansu ke ciki.

Masana harkokin tsaro na ganin cewa hare-haren da ake ci gaba da kai wa makarantu a wasu yankunan Arewa maso Gabas na nuna buƙatar ƙarin matakan tsaro domin kare ɗalibai da cibiyoyin ilimi.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url