Mahukuntan Nijar Sun Sake Tsare Wani Fitaccen Ɗan Jarida
An sake bayyana damuwa kan yanayin ‘yancin aikin jarida a Jamhuriyar Nijar bayan rahotanni sun tabbatar da kama shugaban kamfanin wallafa jaridar Enqueteur, Idrissa Soumana Maiga, da mahukuntan ƙasar suka yi.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun tsare ɗan jaridar, sai dai har zuwa yanzu ba a bayyana takamaiman dalilan da suka kai ga kama shi ba.
Lamarin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yadda ake mu’amala da kafafen yaɗa labarai da kuma ‘yan jarida a ƙasar tun bayan da sojoji suka karɓi mulki.
Masu sa ido kan harkokin siyasa da kare haƙƙin ɗan Adam na cewa an samu ƙaruwa a zarge-zargen da suka shafi takaita ayyukan kafafen yaɗa labarai da kuma tsare wasu da ake ganin suna sukar mahukunta.
Mai fafutukar tabbatar da dimokuraɗiyya a Nijar, Sahnounou Mahamadou, ya bayyana sabon kamen a matsayin wani koma-baya ga ‘yancin aikin jarida da kuma tsarin dimokuraɗiyya.
Ya ce samun damar ‘yan jarida na gudanar da aikinsu ba tare da tsangwama ba na da muhimmanci wajen tabbatar da gaskiya da bai wa al’umma damar samun sahihan bayanai.
Wasu masu sharhi kan harkokin siyasa a yankin kuma sun ce irin waɗannan matakai na iya ƙara haifar da damuwa a tsakanin ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da ƙasashen duniya da ke sa ido kan halin siyasar Nijar.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, mahukuntan Nijar ba su fitar da wata sanarwa a hukumance da ke ƙarin haske kan dalilin tsare Idrissa Soumana Maiga ba.
