APC Ta Lashe Dukkan Kujerun Zaɓukan Ƙananan Hukumomi a Gombe
Jam’iyyar APC ta samu nasarar lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 24 da kuma kujerun kansiloli 240 da aka fafata a zaɓukan ƙananan hukumomi da aka gudanar a jihar Gombe ranar Asabar.
Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Gombe (GOSIEC), Abdullahi Garba Talasse, wanda ya sanar da sakamakon a ranar Asabar a Gombe, ya bayyana cewa jam’iyyar mai mulki ta yi nasara a dukkan ƙananan hukumomi da yankunan bunƙasa ƙananan hukumomi (LCDAs) da aka gudanar da zaɓe a cikinsu.
Talasse ya bayyana nasarar gudanar da zaɓe a sabbin yankunan LCDAs a matsayin wani babban ci gaba a tsarin dimokuraɗiyyar jihar, yana mai cewa Gombe ta ƙaru daga ƙananan hukumomi 11 da kansiloli 114 zuwa ƙananan hukumomi da LCDAs 24 tare da kansiloli 240.
Ya ce hukumar ta yi aiki tare da Majalisar Dokokin Jihar domin samar da duk wata doka da ake buƙata domin gudanar da zaɓukan a sabbin yankunan.
Ya ce:
"Ba mu yi ƙoƙarin samar da dokar da ake buƙata a banza ba. Yau mun samu nasarar gudanar da zaɓe a ƙananan hukumomi da LCDAs 24, wanda babban ci gaba ne ga jihar."
Shugaban GOSIEC ya danganta rashin samun nasarar jam’iyyun adawa da ƙarancin yawan ‘yan takarar da suka tsayar a zaɓen.
A cewarsa, jam’iyyar African Congress (AC) ta tsayar da ‘yan takara ne kawai a kujerun shugabancin ƙananan hukumomi uku, yayin da Democratic Liberation Alliance (DLA) ta shiga takara a ƙananan hukumomi shida.
Ya ƙara da cewa jam’iyyun New Nigeria People’s Movement (NRM), Youth Party (YP) da Zenith Labour Party (ZLP) kowacce ta tsayar da ‘yan takara a kujerun shugabancin ƙananan hukumomi uku.
Dangane da kujerun kansiloli, Talasse ya ce AC ta shiga takara a gundumomi takwas, yayin da DLA, NRM, YP da ZLP suka shiga takara a gundumomi 11 kowacce.
Ya ce hakan ne ya sa wasu jam’iyyu suka samu ƙuri’u sifili a wasu yankuna saboda ba su shiga takara a dukkan ƙananan hukumomi da gundumomi ba.
Daga ƙarshe ya tabbatar da cewa:
"Daga sakamakon da ke gaban hukumar, APC ta lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 24 da kuma kujerun kansiloli 240."
Ya kuma yaba wa jam’iyyun siyasa, masu sa ido kan zaɓe, ƙungiyoyin farar hula, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki bisa gudummawar da suka bayar wajen tabbatar da gudanar da zaɓe cikin lumana.
