A Najeryia Likitocin da ke Horo Sun Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki Idan Buƙatunsu Ba Su Biya Ba



Ƙungiyar Likitocin da ke horo ta Najeriya (NARD) a ranar Asabar ta ayyana cewa tana cikin takun-saka da Gwamnatin Tarayya, tare da tsawaita wa’adin makonni huɗu da ta bai wa gwamnati domin cika buƙatunta da suka rage. Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa za ta iya shiga yajin aiki a faɗin ƙasa idan ba a warware matsalolin ba.

An ɗauki sabon matakin ne a taron gaggawa na Majalisar Zartarwar Ƙungiyar ta Ƙasa (E-NEC), wanda aka gudanar ta yanar gizo a ranar Asabar domin nazartar abubuwan da suka faru bayan ƙarewar wa’adin kwanaki 21 da ta bai wa Gwamnatin Tarayya a baya.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, wadda shugaban ƙungiyar Dakta Mohammad Usman Suleiman da Sakatare Janar Dakta Shuaibu Ibrahim da Sakatare mai kula da yaɗa labarai da harkokin zamantakewa Dakta Abdulmajid Yahya Ibrahim suka sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce ba za ta iya ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a harkokin aiki ba bayan wannan sabon wa’adi na makonni huɗu idan ba a biya mata buƙatunta gaba ɗaya ba.

NARD ta kuma umarci kwamitin shugabanninta da su fara shirye-shiryen da suka dace domin shiga yajin aiki idan gwamnati ba ta nuna gamsasshen mataki wajen cika buƙatun cikin lokacin da aka tsara ba.

Ƙungiyar ta zargi Gwamnatin Tarayya da wasu cibiyoyin lafiya da gaza cika alƙawuran da suka shafi jin daɗin likitoci, ciki har da biyan albashin da ake binsu, alawus-alawus da sauran haƙƙoƙinsu.

Daga cikin matsalolin da har yanzu ba a warware ba, ƙungiyar ta bayyana cewa har yanzu ba a fitar da kuɗaɗen Asusun Horar da Likitoci na shekarar 2026 (MRTF) ba duk da alƙawuran da gwamnati ta yi sau da dama.

Sanarwar ta ce: "NARD ba za ta ci gaba da jure wa wahalhalun da ake dorawa likitoci ba sakamakon jinkirin biyan albashi da sauran haƙƙoƙinsu."

Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan yadda ake muzgunawa wasu mambobinta a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Obafemi Awolowo (OAUTHC) da ke Ile-Ife, tare da yin Allah wadai da yunƙurin sake dawo da kuɗin amfani da kayan aiki ga likitocin da ke horo a wasu cibiyoyin lafiya masu zaman kansu duk da umarnin gwamnati na baya.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url