Dattawan Katsina Sun Bukaci A Saki Dr. Bashir Usman Kurfi Ba Tare da Sharadi Ba
Wasu dattawa a jihar Katsina sun yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta sakin masanin harkokin tsaro kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, Dr. Bashir Usman Kurfi, ba tare da wani sharadi ba.
A cikin wata sanarwa da Dokta Hassan Garba ya sanya wa hannu a madadin ƙungiyar, dattawan sun bayyana cewa ci gaba da tsare Dr. Kurfi na iya kawo cikas ga ƙoƙarin da ake yi na magance matsalolin tsaro a jihar Katsina da ma yankin Arewa maso Yamma.
Sanarwar ta ce Dr. Kurfi ya daɗe yana taka muhimmiyar rawa wajen bayar da shawarwari da bayanan da suka shafi tsaro, tare da haɗin gwiwa da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin yaƙi da 'yan bindiga da sauran ayyukan ta'addanci.
Dattawan sun jaddada cewa irin gudunmawar da Dr. Kurfi ke bayarwa ta taimaka wajen fahimtar hanyoyin da suka dace na tunkarar matsalar rashin tsaro, saboda haka suka bukaci hukumomi su sake nazarin matakin da suka ɗauka a kansa.
Sun kuma yi kira da a tabbatar da bin doka da oda tare da kare haƙƙin 'yan ƙasa, suna mai cewa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, hukumomin tsaro da masana harkokin tsaro na da matuƙar muhimmanci wajen shawo kan matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin da suka tsare Dr. Bashir Usman Kurfi ba su fitar da wata sanarwa a hukumance da ke bayani kan dalilan ci gaba da tsare shi ko martani ga kiran da dattawan suka yi ba.
