Bama-Bamai Biyu Sun Tashi Kusa da Masauƙin Macron Yayin Ziyararsa a Syria
An ji ƙarar fashewar bama-bamai biyu da sanyin safiyar Talata a birnin Damascus, kusa da otal ɗin da shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya sauka yayin wata muhimmiyar ziyara da yake kai wa ƙasar.
Shaidun gani da ido sun ce an ga tiririn hayaƙi na tashi a kusa da otal ɗin Four Seasons da ke tsakiyar Damascus, inda Macron ya kwana tun bayan isowarsa ƙasar a yammacin Litinin.
Gwamnatin Syria ta sanar cewa fashewar ta jikkata mutane 18, ciki har da jami'an 'yan sanda huɗu. Sai dai hukumomi ba su bayyana musabbabin fashewar ba a lokacin fitar da wannan rahoto.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan shugaban na Faransa ya isa fadar shugaban ƙasar domin ganawa da shugaban Syria, Ahmed al-Sharaa, a wani ɓangare na ziyararsa ta hukuma.
Fadar shugaban Faransa ta Elysee ta tabbatar da cewa Macron na cikin ƙoshin lafiya kuma yana ci gaba da gudanar da shirye-shiryen ziyararsa ba tare da wata matsala ba.
Ziyarar Macron na da muhimmanci, domin ita ce ta farko da wani shugaban babbar ƙasar Yammacin Turai ya kai Syria tun bayan sauyin gwamnati da ya kawo Ahmed al-Sharaa kan mulki a shekarar 2024.
Haka kuma, wannan shi ne karon farko cikin kusan shekaru 17 da wani shugaban ƙasar Turai ya kai ziyara Damascus, bayan da rikicin basasar Syria da ya ɓarke a shekarar 2011 ya haifar da katse alaƙar diflomasiyya tsakanin Faransa da gwamnatin Syria ta wancan lokaci.
Masu lura da al'amuran siyasa na ganin cewa, duk da wannan fashewa, ziyarar Macron na nuna sabon yunƙurin ƙasashen Turai na sake gina dangantaka da sabuwar gwamnatin Syria, a daidai lokacin da ƙasar ke ƙoƙarin farfaɗowa daga shekaru masu tsawo na rikici.
