Kotun Tarayya Ta Tabbatar da Shugabancin ADC Karkashin David Mark
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da sahalewar shugabancin jam’iyyar ADC karkashin David Mark, inda ta yi watsi da karar da dan majalisar wakilai Leke Abejide ya shigar domin kalubalantar shugabancin jam’iyyar.
Mai shari’a Musa Liman ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, inda ya amince da bukatun farko da jam’iyyar ADC da tsohon shugaban ta na kasa Ralph Nwosu da David Mark da kuma sakataren jam’iyyar na kasa Rauf Aregbesola suka gabatar.
Kotun ta bayyana cewa ba ta da hurumin sauraron karar saboda tana da alaka da harkokin cikin gida na jam’iyyar siyasa, wadanda a cewar kotun ba su cikin batutuwan da kotu ke shiga kai tsaye.
Haka kuma, kotun ta yanke cewa Leke Abejide bai nuna yadda hakkinsa ya samu tangarda sakamakon nada shugabannin jam’iyyar ba, lamarin da ya sa aka ce ba shi da hurumin shigar da karar.
Mai shari’ar ya kuma bayyana cewa dan majalisar bai fara amfani da hanyoyin warware rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyar ba kafin ya garzaya kotu.
Dangane da sahihancin yadda David Mark da Rauf Aregbesola suka zama shugabannin jam’iyyar, kotun ta bayyana cewa mika shugabancin da Ralph Nwosu ya yi bai saba kundin tsarin mulkin ADC ba.
Kotun ta ce taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar 2 ga Yulin 2025, wanda a cikinsa aka mika shugabanci, ya gudana ne kafin taron Kwamitin Zartarwa na Kasa da aka gudanar a ranar 29 ga Yulin 2025, wanda daga bisani ya tabbatar da David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa da Rauf Aregbesola a matsayin sakatare na kasa a karkashin kulawar Hukumar Zabe ta Kasa, INEC.
Kotun ta kara da cewa tsarin ya yi daidai da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ADC da kuma dokar zabe ta shekarar 2026.
Baya ga haka, kotun ta umarci Leke Abejide ya biya wadanda ake kara kudin shari’a na naira miliyan biyu ga kowane bangare, sannan ta umarci lauyansa ya biya karin naira miliyan goma bisa tanade-tanaden dokar zabe ta 2026.
Tun farko dai Abejide ya bukaci kotu ta soke mika shugabancin jam’iyyar da aka yi a watan Yulin 2025 tare da hana David Mark da Rauf Aregbesola bayyana kansu a matsayin shugabannin ADC, yana mai zargin cewa tsarin nadin nasu bai bi ka’idojin jam’iyyar da dokar zabe ba.
