Aƙalla Mutane 18 Sun Mutu a Sabbin Hare-hare da Ramuwar Gayya a Jihar Neja



Aƙalla mutane 18 ne suka rasa rayukansu a jihar Neja da ke yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya sakamakon jerin hare-hare da ake dangantawa da rikicin manoma da makiyaya da ya dade yana addabar wasu yankunan ƙasar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun samu rahoto daga yankin Katako da ke ƙaramar hukumar Rafi cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari ƙauyen Godoro a daren ranar Litinin.

A cewarsa, maharan sun kashe wani matashi mai shekaru 25 a harin, lamarin da ya janyo mambobin ƙungiyar sa-kai ta yankin suka tare hanya tare da kashe wani mutum mai shekaru 28 a matsayin ramuwar gayya.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma bayyana cewa a wani sabon lamari da ya faru a daren Talata, wasu mutane sun ƙona mutum 15 har lahira a wani gida mai ɗakuna biyu da ke Angwan-Baago kusa da ƙauyen Godoro, yayin da aka kashe wani mutum a wani wuri daban.

Sai dai wasu majiyoyi daga yankin sun ce adadin waɗanda suka mutu na iya kaiwa 48 sakamakon hare-haren da ramuwar gayya da suka biyo baya.

Wani mazaunin yankin, Hamza Maisaje Kwana, ya ce ko da yake ba a tabbatar da cikakken adadin waɗanda abin ya shafa ba, hasashen da suke yi ya nuna cewa mutanen da suka mutu sun fi adadin da aka bayyana a hukumance.

Tashe-tashen hankulan manoma da makiyaya dai sun dade suna haddasa asarar rayuka da dukiyoyi a wasu sassan Najeriya, inda ake danganta su da rikice-rikicen filaye, kiwo da kuma rikice-rikicen ƙabilanci da addini.

Masu ruwa da tsaki na ci gaba da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su dauki matakan gaggawa domin dakile yawaitar irin wadannan hare-hare da kuma samar da zaman lafiya mai dorewa.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url