Sojojin Mali Sun Kashe Mahara Da Dama Bayan Hare-Hare a Sassan Ƙasar
Rundunar sojin ƙasar Mali ta bayyana cewa dakarunta sun samu nasarar kashe mahara da dama bayan wasu hare-hare da aka kai a sassa daban-daban na ƙasar.
Wannan na zuwa ne a lokacin da Mali ke ci gaba da ƙoƙarin daƙile matsalolin tsaro da suka daɗe suna addabar ƙasar, musamman hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce an dawo da kwanciyar hankali a yankunan da aka kai hare-haren bayan da dakarunta suka samu nasarar daƙile su.
Sanarwar ta ce maharan sun kai hare-hare a birane biyar da suka haɗa da Alguel-Hoc da Anéfis da Gao a arewacin ƙasar, da Kenioroba da ke kudancin babban birnin Bamako, sai kuma Sévaré da ke tsakiyar ƙasar.
Rundunar ta bayyana cewa a birnin Sévaré kadai, an kashe mayaƙa 20, yayin da aka kashe wasu shida a Gao.
Sai dai rundunar ta ce ta rasa jami’i guda ɗaya a yayin artabun, yayin da wasu jami’ai huɗu suka samu raunuka.
A halin da ake ciki, ƙungiyar ‘yan aware ta Azawad Liberation Front (FLA) ta ɗauki alhakin kai hare-haren.
Mali dai na daga cikin ƙasashen yankin Sahel da suka dade suna fama da matsalolin tsaro, inda hare-haren ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai suka ci gaba da jefa al’umma cikin fargaba.
