LABARI MAI DUMI: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shugaban Ƙaramar Hukumar Bungudu a Zamfara
Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun yi garkuwa da Shugaban Ƙaramar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara, Hon. Nura Umar Bungudu.
Rahotanni sun ce maharan sun kutsa cikin garin Bungudu a daren ranar Alhamis, inda suka nufi gidan shugaban ƙaramar hukumar da ke unguwar Zango, mai nisan kasa da kilomita 20 daga babban birnin jihar, Gusau.
Wani mazaunin garin da ya yi magana da Daily Trust bisa sharadin a sakaya sunansa, ya ce maharan sun yi galaba a kan jami'an tsaron da ke gadin gidan, inda suka kashe 'yan sanda biyu da 'yan banga biyu, kafin su tafi da shugaban ƙaramar hukumar da wasu daga cikin iyalansa.
Ya ce:
"Sun kashe 'yan sanda biyu da 'yan banga biyu, ciki har da wani ɗan banga mai aikin sa-kai da ya kasance yana taimakawa wajen kare garin daga hare-haren 'yan bindiga."
A cewarsa, jami'an tsaron da ke gidan sun yi ƙoƙarin dakile harin, amma maharan sun fi su ƙarfin makamai.
"'Yan bindigar sun shigo garin da niyyar aiwatar da abin da suka zo yi. Jami'an tsaron shugaban ƙaramar hukumar sun yi turjiya, amma makaman maharan sun fi nasu ƙarfi."
Majiyar ta ƙara da cewa da farko maharan sun yi garkuwa da shugaban ƙaramar hukumar, matarsa da 'ya'yansa.
Sai dai jami'an tsaro da suka bi sawun maharan sun yi nasarar ceto yara huɗu ko biyar daga cikin yaran.
"Sun tafi da shugaban ƙaramar hukumar tare da matarsa da 'ya'yansa, amma daga baya jami'an tsaro sun ceto wasu daga cikin yaran. Abin takaici, shugaban ƙaramar hukumar ya ci gaba da kasancewa hannun maharan."
Ya bayyana cewa duk da an tura ƙarin jami'an tsaro zuwa wurin, sun isa ne bayan maharan sun riga sun tsere.
"Jami'an tsaro sun yi bakin ƙoƙarinsu, amma kafin ƙarin dakaru su iso, 'yan bindigar sun riga sun aiwatar da harin kuma sun tsere."
Mazaunin garin ya danganta yawaitar irin waɗannan hare-hare da makamai masu ƙarfi da 'yan bindigar ke amfani da su, da kuma ayyukan masu ba su bayanan sirri.
"Ba sa bayar da wata alama kafin su kai hari. Suna zuwa da makamai masu ƙarfi kuma da yawa. Duk da ƙoƙarin jami'an tsaro, sun samu damar tafiya da shugaban ƙaramar hukumar."
Ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara ƙarfafa matakan tsaro a Bungudu da sauran yankunan da ke fuskantar irin waɗannan hare-hare.
"Al'ummarmu sun haɗa kai da jami'an tsaro wajen yin turjiya, amma 'yan bindigar sun fi su ƙarfin makamai. Muna roƙon gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin jama'a."
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ƙoƙarin samun tabbacin hukuma daga Rundunar 'Yan Sandan Jihar Zamfara bai yi nasara ba, domin ba a samu amsa daga kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ba kan kiran waya da saƙon tes da aka aika masa.
