Jami'an Tsaro 15 Sun Mutu Bayan Harin Ɗan Kunar Bakin Wake a Pakistan
Akalla jami'an tsaro 15 ne suka rasa rayukansu bayan wani ɗan kunar bakin wake tare da rakiyar wasu 'yan bindiga suka kai hari kan wani shingen binciken jami'an tsaro a garin Tank da ke lardin Khyber Pakhtunkhwa a arewa maso yammacin Pakistan.
A cikin wata sanarwa da Rundunar Sojin Pakistan ta fitar ranar Juma'a, ta ce jami'anta sun yi nasarar dakile harin da aka kai da daddare, inda suka kashe mayaƙa 12 bayan musayar wuta mai tsanani.
Rundunar ta ɗora alhakin kai harin kan ƙungiyar Tehrik-e-Taliban Pakistan (TTP), wadda ta dade tana kai hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula a ƙasar.
Ko da yake TTP ba ita ce ƙungiyar Taliban da ke mulki a Afghanistan ba, ana ganin ƙungiyoyin biyu na da alaƙa ta akida da tarihi.
A tsawon lokaci, Pakistan na zargin gwamnatin Taliban ta Afghanistan da bai wa mayaƙan TTP mafaka a kan iyakar ƙasashen biyu, sai dai gwamnatin Kabul ta ci gaba da musanta waɗannan zarge-zarge.
Harin na baya-bayan nan ya sake nuna irin ƙalubalen tsaro da Pakistan ke fuskanta, musamman a yankunan da ke makwabtaka da Afghanistan, inda hare-haren masu ɗauke da makamai suka ƙaru a cikin 'yan shekarun nan.
