Shugaban Kasar Bangladesh Mohammed Shahabuddin Ya Yi Murabus Saboda Rashin Lafiya
Shugaban ƙasar Bangladesh, Mohammed Shahabuddin, ya yi murabus daga mukaminsa, inda ya bayyana cewa tabarbarewar lafiyarsa ce ta tilasta masa ɗaukar wannan mataki.
Shahabuddin ya tabbatar da murabus ɗin da kansa ga kamfanin dillancin labarai na AFP, yana mai cewa ya yanke shawarar ne bisa raɗin kansa.
A cikin wasiƙar murabus da ya aikewa kakakin Majalisar Dokokin ƙasar, shugaban ya bayyana cewa matsalolin lafiyar jikinsa da ta kwakwalwarsa sun hana shi ci gaba da sauke nauyin da ke kansa.
Shahabuddin, wanda ake kallonsa a matsayin na kusa da tsohuwar Firaminista Sheikh Hasina, ya sauka daga mukamin ne kafin cikar wa'adinsa, wanda aka tsara zai ƙare a shekarar 2028.
Murabus ɗin ya zo ne a lokacin da Bangladesh ke ci gaba da fuskantar sauye-sauyen siyasa bayan rikice-rikicen da suka biyo bayan gwamnatin Sheikh Hasina.
Masana siyasa na ganin sauyin na iya buɗe sabon babi a siyasar Bangladesh, yayin da ake sa ran hukumomin ƙasar za su bi tanade-tanaden kundin tsarin mulki wajen cike gurbin shugaban ƙasar.
