Arewa Ta Rasa Darajojinta da Alkiblarta....In Ji Farfesa Ango Abdullahi.



 Fitaccen dattijon Arewa kuma jagoran kungiyar Northern Elders Forum (NEF), Farfesa Ango Abdullahi, ya bayyana cewa Arewa ta rasa darajojinta da alkiblarta, yana mai cewa matsalolin da yankin ke fuskanta a yau sun samo asali ne daga gazawar shugabanci da kuma kauce wa kyawawan dabi'un da aka gada daga magabata.

Ango Abdullahi ya bayyana hakan ne yayin taron tunawa da marigayi Janar Hassan Usman Katsina da aka gudanar a Arewa House da ke Kaduna. Ya ce idan Arewa ba ta kauce daga darajojinta na gaskiya, riƙon amana da sadaukarwa ba, da ba za ta tsinci kanta a halin da take ciki a yau ba.

Ya jaddada cewa ci gaban kowace al'umma ba ya ta'allaka ga gine-gine ko kayayyakin more rayuwa kaɗai, sai dai yana fara ne da nagartaccen shugabanci da kyawawan ɗabi'u.

Farfesan ya yi kira ga shugabannin Arewa da al'ummar yankin da su yi nazari kan tarihin yankin tare da dawo da kyawawan dabi'un da suka gina martabar Arewa a baya, yana mai cewa hakan ne zai taimaka wajen fuskantar ƙalubalen tsaro, tattalin arziki da ci gaban al'umma.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url