Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Rajistar WAEC da NECO


Daga Muhammad Al-Amin

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO na shekarar 2027, tana mai cewa za ta fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki kafin ɗaukar kowane mataki.

A cikin wata sanarwa, Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya ta bayyana cewa ta janye wasiƙar da ta fitar a ranar 18 ga Yuni, 2026, wadda ke sanar da shirin sake duba kuɗin rajistar jarabawar.

Ma'aikatar ta ce shawarar ƙara kuɗin ta samo asali ne sakamakon hauhawar kuɗin gudanar da jarabawa, ciki har da kuɗin tsaro, jigilar kayan aiki, buga takardun jarabawa, amfani da fasahar zamani da sauran ayyukan tabbatar da inganci.

Sai dai ta ce bayan korafe-korafe da damuwar da jama'a suka nuna, Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, ya ba da umarnin dakatar da shirin domin gudanar da cikakkiyar tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki.

A cewar ma'aikatar, za a yi shawarwari da hukumomin WAEC da NECO, ma'aikatun ilimi na jihohi, masu makarantu, ƙungiyoyin iyaye, ƙungiyoyin ƙwadago da sauran masu ruwa da tsaki kafin a yanke hukunci.

Ta jaddada cewa ba za a aiwatar da wani ƙarin kuɗin rajistar jarabawar ba har sai an kammala wannan tsari.

Masana ilimi sun ce dakatar da shirin na iya rage damuwar iyaye da ɗalibai, musamman a wannan lokaci da ake fama da hauhawar farashin kayayyaki, tare da ba gwamnati damar cimma matsaya da za ta kasance mai adalci ga kowa.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url