Kotu Ta Ba da Umarnin Kama Mutumin da Ya Yi Ikirarin Jagorantar Hukumar PFIPC Kan Zargin Damfara da Satar Takardu

 

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin kamo Adeniyi Adeyemi, wanda ke ikirarin shi ne Darakta Janar na wata hukuma mai suna Presidential Foreign Investment Promotion Council (PFIPC), bayan ya gaza bayyana a gaban kotu domin fuskantar shari'ar da ake masa kan zargin damfara, yin jabun takardu da kuma yin ƙarya da sunan wata hukuma.

Adeyemi ya kamata ya bayyana a gaban Mai Shari'a Mohammed Umar domin a karanta masa tuhume-tuhume takwas da ake yi masa, amma bai halarci zaman kotun ba.

Shari'ar mai lamba FHC/ABJ/CR/562/2025 ta shiga zaman sauraro a ranar Talata ba tare da wanda ake tuhuma ya bayyana ba, lamarin da ya sa Mai Shari'a Umar ya bayar da sammacin kama shi.

An shigar da ƙarar ne tun ranar 27 ga Nuwamban 2025 ta hannun mai gabatar da ƙara daga rundunar 'yan sanda, Wisdom Madaki. Baya ga Adeyemi, akwai wasu mutane biyu da ake tuhuma a cikin shari'ar.

Ana sa ran masu gabatar da ƙara za su gabatar da shaidu da dama yayin shari'ar, ciki har da Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, da wasu jami'an gwamnati da na rundunar 'yan sanda domin tabbatar da zarge-zargen da ake yi.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url