Kotun Tarayya Ta Ba da Umarnin Ƙwace Kadarori 57 da Ake Alaƙanta wa Tsohon AGF Abubakar Malami
Abuja – Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin ƙwace har abada kadarori 57 da ake alaƙanta wa tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami.
Mai shari'a Joyce Abdulmalik ta yanke hukuncin ne bayan amincewa da ƙarar da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta shigar, tana neman a mayar da kadarorin mallakin Gwamnatin Tarayya.
Kotun ta bayyana cewa waɗanda ake ƙarar sun kasa gabatar da hujjojin da za su karya zargin EFCC cewa an mallaki kadarorin ne ta hanyar da ba ta dace ba.
Kafin yanke hukuncin, kotun ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafe da buƙatun da Malami, wasu 'yan uwansa da kuma wasu kamfanoni da ake alaƙanta da kadarorin suka gabatar, tana mai cewa ba su da ingantaccen tushe.
Rahotanni sun nuna cewa EFCC ta shigar da ƙarar ƙwace kadarorin ne tun a watan Janairun 2026, inda ta bayyana cewa kadarorin 57 ɗin, waɗanda darajarsu ta kai kimanin Naira biliyan 212.8, ana zargin sun samo asali ne daga haramtattun ayyuka.
Tun a ranar 16 ga Janairun 2026, Mai shari'a Emeka Nwite ya bayar da umarnin ƙwace kadarorin na wucin gadi tare da umartar EFCC ta wallafa sanarwar a wata jarida ta ƙasa domin bai wa duk wanda ke da wata da'awa a kan kadarorin damar gabatar da hujjoji kafin a yanke hukunci na ƙarshe.
Da hukuncin na ranar Laraba, kotun ta tabbatar da ƙwace kadarorin baki ɗaya, lamarin da ya mayar da su mallakin Gwamnatin Tarayyar Najeriya.
