Dakarun Soji Sun Dakile Yunkurin ISWAP na Sace Dalibai a Monguno, Sun Ceto Dalibai 46 yayin da 'Yan Ta'addan Suka Tsere

Daga: Mohammed Al-Amin

Dakarun Operation HADIN KAI (OPHK) tare da haɗin gwiwar jami'an Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ta MOPOL, sun dakile wani yunƙurin sace ɗalibai da ake zargin mayaƙan ISWAP sun yi a Kwalejin 'Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya (FGGC) da ke Monguno a safiyar Asabar, inda suka ceto ɗalibai 46.

Majiyoyin sirri sun shaida wa Zagazola Makama cewa, 'yan ta'addan sun kutsa cikin makarantar da misalin ƙarfe 1:30 na safiyar ranar 19 ga Yuli, bayan da ake zargin sun samu shiga ne da taimakon wasu da ake zargi suna ba su bayanai ko haɗin kai.

Makarantar, wadda gwamnatin jihar Borno ke amfani da ita a halin yanzu a matsayin masaukin wucin gadi ga ɗaliban Federal Polytechnic Monguno, ta fuskanci harin ne yayin da 'yan ta'addan suka yi yunƙurin yin garkuwa da ɗaliban.

Jami'an tsaro da ke gadin makarantar sun gaggauta buɗe musu wuta, yayin da Rundunar Gaggawa ta Sector 3 (Quick Reaction Force - QRF) ta isa wurin cikin gaggawa domin ƙarfafa tsaro. Wannan haɗin gwiwar ya tilasta wa 'yan ta'addan janye harin tare da tserewa ba tare da yin garkuwa da ko da ɗalibi guda ba.

Majiyoyin sun ce wasu sassan gine-ginen makarantar sun lalace sakamakon musayar wuta, amma jami'an tsaro sun yi nasarar shawo kan lamarin tare da hana abin da ka iya zama babban harin sace ɗalibai.

Bayan kammala aikin, an ceto ɗaliban 46 tare da kwashe su zuwa Barikin Sojoji na Kinnasara da ke Monguno, inda aka yi musu gwaje-gwajen lafiya tare da ba su kulawar da ta dace. An tabbatar da cewa dukkansu suna cikin ƙoshin lafiya.

Sai dai, Zagazola Makama ya gano cewa, abin takaici, wasu ɗalibai sun rasa rayukansu bayan da harsasan da suka kauce wa hanya daga bindigogin 'yan ta'addan da ke gudu suka same su yayin musayar wutar.

Hukumomin soji sun jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, tare da tabbatar da cewa an ƙara tsaurara matakan tsaro a makarantu da sauran muhimman wurare a duk faɗin Arewa maso Gabas.

Sojojin sun kuma bayyana cewa ana ci gaba da bincike domin gano tare da cafke waɗanda ake zargin sun taimaka wajen kai harin, yayin da dakaru tare da sauran hukumomin tsaro suka ƙaddamar da farautar 'yan ta'addan da suka tsere.

A ƙarshe, Operation HADIN KAI ta sake jaddada aniyarta na ci gaba da kai hare-haren murƙushe 'yan ta'adda da kuma tabbatar da tsaron makarantu da al'ummomin Arewa maso Gabas daga duk wani hari a nan gaba.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url