‘Yan Sandan Yobe Sun Ceto ‘Yan Mata Hudu da Aka Yi Garkuwa da Su a Fika



Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta tabbatar da ceto wasu ƙananan ‘yan mata guda huɗu da aka yi garkuwa da su a wani yunkurin satar mutane da ya faru a ƙaramar hukumar Fika ta jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya fitar kuma ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta bayyana cewa a ranar 28 ga watan Yuni, shekarar 2026, ofishin ‘yan sanda na Fika ya samu kiran gaggawa da ke nuna cewa wasu mutane da ba a tantance ko su wanene ba sun kai hari a ƙauyen Didim tare da yin garkuwa da wasu ‘yan mata huɗu.

A cewar rundunar, dukkan waɗanda aka sace ‘yan mata ne ƙanana masu shekaru tsakanin 15 zuwa 17.

Sanarwar ta ce bayan samun bayanin lamarin, jami’an ‘yan sanda da ke aiki a ofishin Kukar Gadu tare da haɗin gwiwar jami’an sintiri na sa-kai sun gaggauta bazama domin gudanar da aikin ceto.

Rundunar ta ƙara da cewa an tura ƙarin jami’ai daga Fika domin ƙarfafa aikin, lamarin da ya kai ga samun nasarar ceto dukkan ‘yan matan ba tare da sun ji wani rauni ba.

Bayan ceton nasu, an garzaya da su cibiyar kula da lafiya ta farko da ke Kukar Gadu domin duba lafiyarsu tare da ba su kulawar da ta dace kafin daga bisani a mayar da su hannun iyalansu.

Sai dai rundunar ta ce har yanzu ana ci gaba da kokarin kamo waɗanda ake zargin suna da hannu a harin bayan da suka tsere daga wurin.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Yobe, CP Usman Kanfani Jibrin, ya umarci jami’an tsaro da su ci gaba da gudanar da ayyukan bincike tare da amfani da bayanan sirri domin kamo masu hannu a lamarin tare da tabbatar da sun fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.

Ya kuma bukaci al’umma da su ci gaba da sanya ido tare da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai kan duk wani motsi ko mutum da ake zargi domin taimakawa kokarin tabbatar da tsaro a jihar.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url